IQNA

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama Ta HRW Ta Bukaci A Saki Sheikh Ibrahim Zakzaky

23:12 - December 15, 2016
Lambar Labari: 3481038
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Right watch ta bukaci gwamnatin Nigeria ta saki shiekh Ibrahim El-Zakzaky shugaban yan shia na kungiyar harka islamia ko kuma Isalamic Movement in Nigeria IMN a takaice.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Pess TV cewa, Kungiyar ta bayyana haka ne a jiya laraba ta kuma bukaci gwamnatin Nigeria ta mutunta hukuncin babban kotu a kasar na sakin malamin da kuma biyansa diyya da shi da matarsa.

MrMausi Segun, babban mai bincike a cikin kungiyar ya kara da cewa akwai bukatar gwamnatin tarayyar kasar ta hukunta duk wadanda suke da hannu a cikin kissan yayan wannan kungiyar a cikin watan Decemban shekarar da ta gabata sannan ta bada umurnin a dakatar da takurawa yan kungiyar.

Kungiyar human Right watch dai ta kammala ta cewa ta dau wannan matakin na kiran gwamnatin Nigeria ta sake malamin ne bayan da rahoton kimitin binciken da gwamnatin jihar kaduna ta kama ta tabbatar da hannu da kuma laifin jami'an tsaro kan kisan kiyashin da aka yiwa yayan wannan kungiyar a ranar 12-14 ga watan Decemban bara.

A cikin watan da ya gabata ne gwamnatin jihar Kaduna a arewacin kasar ta sha alwashin gurfanar da shugaban kungiyar ta IMN kan zargin take doka wanda kungiyarsa ta yi ta yi a cikin shekaru kimani talatin da suka gabata.

Gwamnatin jahar Kaduna ta tabbatar da cewa an rufe gawawwakin yan shi’a dari uku da arbain da bakwai daga cikin wadanda sojoji suka kasha a rikin Zaria acikin ramin guda, amma mabiya harkar musulnci sun adadin ya wuce haka nesa ba kusa ba, inda suka bayar jerin sunayen mutane kusan dubu daya da suka tabbatar da cewa sojoji sun kashe su.

  1. 3554160

captcha