Wasu daga cikin kafafen yada labarai a Najeriya sun ambato wadanda suka shaida lamarin na cewa ana kan yi wa ginin kwaskwarima saboda hasashen cewa jama'a da dama za su halacci taron.
An sa ran Gwamnan jihar Udom Emmanuel zai halarci taron, amma rahotanni sun ce ba ya wurin lokacin da hadarin ya faru.
Rahotannin sun tabbatar da cewa an garzaya da wadanda suka ji raunuka zuwa asibitoci da dama a fadin birnin.
Ana yawan samun ruftawar gine-gine a Najeriya, abin da masu sharhi ke alakanta wa da rashin bin doka da amfani da kayan aiki marasa kyau.
Mutane da dama ne suka mutu a watan Satumbar 2014 lokacin da wani ginin ya rufta a unguwar Lagon da ke cikin birnin Lagos.