IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Za Ta Yi Zaman Gaggawa Kan Sake Tozarta Kur’ani Da Aka Yi

15:33 - July 22, 2023
Lambar Labari: 3489518
Bagadaza (IQNA) ma'aikatar harkokin wajen kasar Iraki ta sanar da cewa an yanke shawarar gudanar da taron gaggawa na ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi dangane da keta alframar kur'ani mai tsarki.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, Ma'aikatar harkokin wajen Iraki ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, wannan taron na da nufin samar da hanyoyin na hadin gwiwa don fuskantar kyamar musulunci a mataki na ƙasa da ƙasa.

A cikin wannan yanayi, ta yi kira ga kasashen duniya da su tashi tsaye wajen aiwatar da ayyukan da suka rataya a wuyansu cikin daidaito, kamar yadda kudurorin kasashen duniya suka tanada.

Da safiyar yau ne ma'aikatar harkokin wajen Iraki ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan laifin da aka aikata na tozarta kur'ani mai tsarki da tutar jamhuriyar Iraki a gaban ofishin jakadancin Irakin da ke Denmark.

Ma'aikatar ta tabbatar da cewa tana bibiyar abubuwan da suke faruwa sau da kafa na cin zarafin musulunci da abubuwa masu tsarki na addini da sunan ‘yancin bayyana ra’ayi ko fadar albarkacin baki a wasu kasashen turai.

Hakan na zuwa ne bayan da wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta kasar Denmark a jiya, ta kona kur'ani mai tsarki a gaban ofishin jakadancin Iraki da ke babban birnin kasar Copenhagen.

Kuma a ranar Alhamis din da ta gabata, Silwan Momica ya yayyaga kwafin kur’ani da tutar kasar Iraki a gaban ofishin jakadancin Bagadaza da ke Stockholm, a wani lamari na biyu da ya faru da wannan mutum ya aikata bayan na farko a karshen watan Yuni, bayan da hukumomin kasar Sweden suka ba shi damar yin hakan a hukumance.

 

 

4157135

 

 

captcha