Kamar yadda majiyar yada labarai ta ofishin Jagoran juyin juya halin Musuluncin ta bayyana cewa, sakon Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei shi ne kamar haka:
da sunan Allah
Yin cin zarafi da tozarci a kan kur'ani mai tsarki a kasar Sweden lamari ne mai daci, makirci da hadari. Mafi tsananin hukunci ga wanda ya aikata wannan aika-aika shi ne abin da dukkanin malaman addinin Musulunci suka hadu a kansa, ya kamata gwamnatin kasar Sweden ma ta san cewa, ta hanyar goyon bayan mai laifi, ta dauki matakin yaki da duniyar musulmi, tare da janyo kiyayyar al'ummomin musulmi da kuma da dama daga cikin gwamnatocinsu.
Aikin wannan gwamnati shi ne mika wanda ya aikata laifin ga hukumomin shari'a na kasashen musulmi. Haka nan ma’abota makirci a bayan fage su sani cewa tsarki da daukaka ta kur’ani mai girma za su rika karuwa a kowace rana kuma hasken shiriyarsa za su rika haskakawa, irin wannan makirci da masu yinsa sun kaskanta, da ba za su iya hana wannan haske ci gaba da kara yaduwa ba. Allah ne mai rinjaye a kan lamarinsa.
Sayyid Ali Khamenei
22 Yuli 2023