IQNA

A Lebanon an gudanar da zanga-zangar la'antar Sweden kan sake kona kur'ani a kasar

16:51 - July 21, 2023
Lambar Labari: 3489515
Beirut (IQNA) A yau 21 ga watan Yuli ne aka gudanar da zanga-zangar la'antar sake kona kur'ani a kasar Sweden bayan sallar Juma'a a yankunan kudancin birnin Beirut da ma wasu yankuna na kasar Lebanon.

Tashar Al-Mayadeen ta bayar da rahoton cewa, al'ummar yankin "Dahiya" da ke kudancin birnin Beirut, sun amsa bukatar Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon, a yammacin jiya Alhamis, kuma bayan sallar Juma'a, sun taru a gaban masallatai a wannan yanki, inda suka yi Allah wadai da matakin da kasar Sweden ta dauka na ba da izinin sake kona kur'ani.

 Masu zanga-zangar na kuma rike da kwafin kur’ani mai tsarki da kuma allunan da ke jaddada korar jakadan Sweden daga Lebanon.

A halin da ake ciki, an dauki tsauraran matakan tsaro a yankin da ke kusa da ofishin jakadancin Sweden da ke birnin Beirut.

Har ila yau masu zanga-zangar na Lebanon sun yi yunkurin kona tutar kasar Sweden, kuma a kudancin kasar Lebanon mazauna wannan yanki sun gudanar da tarurrukan zanga-zangar yin Allah wadai da matakin da hukumomin Sweden suka dauka na ba da izinin kona kur'ani a hukumance.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Lebanon ita ma ta fitar da wata sanarwa a safiyar yau 21 ga watan Yuli inda ta yi Allah wadai da matakin da mahukuntan kasar Sweden suka dauka na ba da izinin kona Kalmar Wahayi tare da daukar hakan a matsayin ci gaba da keta ji da mutuncin musulmi.

Hakazalika masu zanga-zangar kasar Iraki sun gudanar da wata zanga-zanga a birnin Divanieh domin nuna adawa da wulakanta kur'ani mai tsarki, yayin da a yau ma garuruwa daban-daban na jamhuriyar Musulunci ta Iran suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da sake kona kur'ani a kasar Sweden.

Salvan Momika dan kasar Sweden dan asalin kasar Iraki, wanda ya kona kur'ani mai tsarki a ranar farko ta bikin sallar Idi, ya sake cin zarafin kur'ani da tutar kasar Iraki a gaban ofishin jakadancin kasar da ke Stockholm, a ranar Alhamis 20 ga watan Yuli, wanda kuma ke karkashin kariyar 'yan sandan kasar Sweden.

 

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4156811

captcha