IQNA

Mus'hafi na farko mai rubutun ayoyi da aka dinka da zare a wajen baje kolin littafai na Alkahira

23:13 - February 03, 2022
Lambar Labari: 3486903
Tehran (IQNA) an nuna wani kwafin kur'ani a baje kolin littafai na Alkahira wanda aka rubuta shi ta hanyar dinka ayoyinsa da zare.
Mus'hafi na farko mai rubutun ayoyi da aka dinka da zare  a wajen baje kolin littafai na Alkahira

"Mohammad Maher Hazeri", wani masanin mai aikin fasaha dan kasar Syria da ke zaune a kasar Turkiyya, ya fara aikin mushafi na ayoyi na farko da aka yi rubutunsa ta hanyar dinkii da zare tun shekara ta 2000, kuma a cewarsa, an kwashe shekaru 12 ana aikin kafin kammala shi.

Wannan aiki mai ban sha'awa wanda ya ja hankalin maziyartan baje kolin littafai na birnin Alkahira da hazakarsa ta musamman, ya yi wani aiki na daban da keken dinki, ya kuma yi wa ayoyin kur'ani mai tsarki aiki na fasaha da zare mai kalolin zinare da azurfa.

Hazari ya ce an shirya wannan Mus'hafi ne a mujalladi 12 a cikin nau'in rubutun Uthman Taha kuma tsawonsa 80cm, fadinsa cm 60, nauyinsa kilogiram 200 ne, kowane juzu'i kashi biyu da rabi ne.

Ya zuwa yanzu dai ya baje kolin ayyukansa a kasashe daban-daban da suka hada da Iran, Syria, Lebanon, Kuwait, UAE, Qatar da kuma bana a birnin Alkahira.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4033572

captcha