IQNA

James P. Farwell: Akwai Abubuwa Da Saudiyya Ke Tsoro Idan Aka Kawo Karshen Yakin Yemen

22:54 - February 06, 2021
Lambar Labari: 3485624
Tehran (IQNA) Ba’amurke masani kan harkokin siyasar yankin gabas ta tsakiya ya bayyana cewa, akwai abubuwa da Saudiyya take ji am tsoro idan aka kawo karshen yakin Yemen.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna, James P. Farwell dan kasar Amurka kuma masani kan harkokin siyasar yankin gabas ta tsakiya, ya bayyana cewa, akwai abubuwa wadanda gwamnatin Saudiyya take ji ma tsoro idan har aka kawo karshen yakin kasar Yemen.

Ya ce daga cikin abubuwan da take ji ma tsoro har da abin da zai biyo baya a kasar, ta yadda ita ta riga ta rasa duk wani tasiri da a da take da shi, inda a da mutanen kasar suna kallonta a matsayin babbar kasar musulmi, amma yanzu bayan kisan gillar da ta yi a kansu, wannan ya zo karshe.

Na biyu kasashen ad suka taimaka ma al’ummar kasar Yemen a cikin irin wannan mawuyacin halin, su ne za su zama masu kima a wajen al’ummar kasar Yemen, daga cikin wadannan kasashe kuwa akwai wadanda gwamantin Al saud ke kallonsu a matsayin abokan hamayya, kamar irin su Iran.

Baya ga haka kuma a cewar wannan masani, akwai wani babban batu wanda yafi komai daga hankali, shi ne batun bin kadun abin da ya faru koda kuwa bayan wasu shekaru ne masu zuwa, wanda tabbas sai a tayar da wanann batu, shi ne bincike kan laifukan yaki da kisan bil adama da gwamnatin saudiyya ta yi a kasar Yemen.

Dauko irin wannan batu ba a bu ne da zai faranta ran mahukuntan al saud ba, musamman ganin cewa sun dogara ne ga Amurka domin samun kariya, wanda kuma a kowane lokaci ana samun sauye-sauye a kasar amurka, ba dole ne a samu gwamnatin da za ta bas u kariya a kan dukkanin laifukan da suka aikata ba.

Wani abu wanda zai fi sauki a matsayin misali kan hakan, kisan dan jaridar kasar da suka yi, wanda gwamnatin da ta gabata aAmurka ta hana a yi bincike kan hakan, yanzu kuma bayan faduwa wannan gwamnati, sabuwar gwamnatin da ta zo a Amurka tana neman dauko wannan batu, wanda ko alama ba zai yi ma mahukuntan masarautar al Saud dadi ba, domin kuwa hakan zai iya kai wasu daga cikinsu a kotun manyan laifuka ta duniya, wanda kuma tabbas batun Yemen ma zai kaisu ga haka a wata rana.

3951836

 

 

captcha