IQNA

A Yau Ne Ake Gudanar Da Tarukan Ranar Hijabi Ta Duniya

14:18 - February 01, 2021
Lambar Labari: 3485609
Tehran (IQNA) Yau ce ranar hijabi ta duniya, ranar da mata musulmi a ko’ina cikin fadin duniya sukan gudanar da taruka domin muhimmancin hijabi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, kamar yadda aka saba a shekarun baya a kowace ranar 1 ga watan Fabrairu mata musulmi a ko’ina cikin fadin duniya su kan gudanar da taruka domin muhimmancin hijabi,a  yau ana gudanar da irin wadannan taruka.

A baya a wannan rana ana gudanar da manyan taruka a dakunan taruka a birane daban-daban na kasashen duniya, da kuma masallatai gami da cibiyoyi na addini da na al’adu, inda a kan gabatar da bayanai kan matsayin hijabi a cikin addinin muslunci da kuma hikimar da ke tattare da saka shi.

A shekarar bana saboda yanayin da ake ciki, wanna yasa a kasashe da dama ba za a gudanar da taron ta hanyar taruwar jama’a wuri guda ba, mafi yawan kasashen tarukan za su gudana ne ta hanyar hotunan bidiyo na yanar gizo.

A ranar hijabi ta duniya mata suna saka nau’o’in hijabi wanda shi ne suura ta muslunci da ke rufe jiki ga mata, da wayar da kai kan muhimmancin hijabi da kuma matsayinsa  a cikin addinin muslunci.

Haka nan kuma mata sukan bayar da kyautuka na musamman ga ‘yan uwansu mata wadada ba musulmi ba, tare da gayyatarsu zuwa gidajensu  ko kuma wasu wuraren taruka na musamman da ake shiryawa a ranar kan hijabi.

A kan bayar da hijabi ga masu bukata domin sakawa a wannan ranar, domin su ji yadda musulmi suke ji, domin su gane cewa hijabi tufafi ne ba wani abin tsoro ba ne, domin su daina yi wa musulmi mata masu yin lullubi wani kallo na daban.

Dukkanin  addinai da aka saukar daga sama dai sun yi umarni da saka hijabi, kamar yadda addinin musulunci da ya zo karfafa wannan lamari  kamar yadda yake a  sauran addinai da aka saukar daga sama.

An fara gudanar da ranar hijai ne cikin shekara ta 2013 a kasar Amurka, sakamkon cin zarafin da mata musulmi masu saka lullubi suke fuskata daga wasu masu kyamar musulunci a kasar.

A wanann shekarar ma an yi ta bayar da sanarwa a kan yadda wadannan taruka za su gudana a kasar ta Aurka da kuma gayyatar wadanda ba musulmi da su shiga cikin manhajar da za a yi amfani da ita ta yanar gizo a cibiyoyin muuslmi daban-daban da ke kasar.

3951098

 

captcha