IQNA

Sheikhul Azhar: Kiran Musulunci Da Addinin Ta'addanci Jahilci Ne Babba

22:19 - October 21, 2020
Lambar Labari: 3485295
Tehran (IQNA) Babban malamin Azhar ya bayyana jingina ayyukan ta’addanci da addinin muslunci da wasu ke yi a matsayin babban jahilci dangane musulunci.

A cikin wani bayani day a fitar wanda aka yada a cikin harsunan larabci da kuma turancin Ingilishi da Faransanci, Sheikh Ahamd Tayyib babban malamin cibiyar Azhar a kasar Masar ya bayyana cewa, abin takaici ne yadad wasu suke ta hankoron bayyana addinin muslunci a matsayin addinin ta’addanci.

Ya ce babu wani dalili da zai sanya ayyukan wasu daga cikin musulmi su zama abin da za a hukunta addinin musulunci da shi, yin haka ba adalci ba ne a hankalce, domin kuwa  a cikin kowane addini da kowane irin lamari akwai masu tsatsauran ra’ayi da wuce gona da iri, saboda haka ba a hukunta dukkanin addinai da ayyuka na irin wadannan mutane ba.

Malmin ya yi ishara da kyakyawar koyarwa ta addinin muslunci, da hada da girmama dan adam da mutunta shi da kyautata masa, kamar yadda kuma bai yardsa da cin zarafin dan adam ko da kuwa ba musulmi ne ba, kuma tarihin muslunci da rayuwar ma’aiki (SAW) sun tabbatar da haka.

Ya kara da cewa, babban abin da yake da muhimanci shi ne dukkanin bangarori su dauki matakai na taka burki ga wadanda suke wuce gona da iri, domin kuwa wasu lokuta ayyukan wasu na tsokana da tozarci ga wasu ne ke jawo wasu matsalolin da za su cutar da kowa.

3930284

 

captcha