IQNA

Jerin Gwano A Indiya Domin Adawa Da Ziyarar Trump A Kasar

23:55 - February 25, 2020
Lambar Labari: 3484559
Mutane bakwai sun mutu a yayin jerin gwanon kin jinin Donald Trump a birnin New Delhi.

Rahotanni daga India na cewa firai ministan kasar India Narendra Modi ya tarbi Donald Trump na kasar Amurka a jiya a birnin New Delhi, a daidai lokacin da dubun-dubatar al’umma suke gudanar da gagarumar zanga-zanga a babban birnin kasar.

Manufar jerin gwanon dai ita ce nuna adawa sabuwar dokar kasar wadda take nuna wa musulmi wariya a zahiri, da kuma neman mayar da su saniyar ware a kasar, amma daga bisani ta rikide ta koma zanga-zangar la’anatar shugaban Amurka da kuma yin tir da ziyararsa a kasar tasu.

Ministan harkokin cikin gida na kasar India ya bayyana cewa, wadanda suka gudanar da zanga-zangar babbar manufarsu ita ce bakanta fuskar kasar, domin kuwa zanga-zangar ta zo a daidai lokacin da Trupm yake ziyartar kasar.

Gwamnatin India ta sanar da cewa, za ta bayar da izinin zama dan kasa ga ‘yan asalin kasashen Afghanistan, Pakistan da kuma Bangaladash ne da suke zaune a India tun kafin shekara ta dubu biyu da sha hudu  amma mabiya addinan Hindus, Sik, Buda da kuma kiristoci, amma banda musulmi, almarin da ke kasar ta India ke ci gaba da shan kakkausar suka a kansa daga kungiyoyin masu fafutuka.

 

3881345

 

captcha