IQNA

Dakarun Yemen Sake Kai Harin Ramuwar Gayya Kan Kamfanin ARAMCO

23:56 - February 21, 2020
Lambar Labari: 3484546
Tehran – (IQNA) dakarun kasar Yemen sun sake kaddamar da wasu hare-haren mayar da martani kan kamfanin ARAMCO na masarautar Saudiyya.

Shafin almasirah net ya bayar da rahoton cewa, Brigadier janar Yahya Sari ya bayyana cewa, da jijjifin safiyar yau Juma’a dakarun kasar Yemen gami da dakarun sa kai na kabilun larabawan kasar sun kai harin mayar da martani kan ARAMCO da wasu muhimman wurare na masarautar Al Saud.

Yahya Sari ya ce, wannan harin ramuwar gayya ya zo ne kwanaki uku bayan kisan kiyashin da Saudiyya ta yi a kan mata da kananan yara a garin Jauf, bayan da jiragenta suka kaddamar da munanan hare-harea  kan gidajen jama’a fararen hula.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, lokaci ya wuce wanda masarautar Al Saud za ta ci karenta babu babbaka a kan al’ummar kasar Yemen, matukar ta ci gaba da kai hare-hare, to tabbas ta saurari mayar da martani a kan muhimman wurarenta na tattalin arziki.

 

3880427

 

captcha