IQNA

Angela Markel Ta Yi Allawadai Da Nuna Wariya A Jamus

23:39 - February 20, 2020
Lambar Labari: 3484543
Tehran - (IQNA) shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta yi Allawadai da harin da wani ya kai ya kashe mutane 9 a kasar.

Shafin yada labarai na tasha alamanar ya bayar da rahoton cewa, hugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta yi Allawadai da harin da wani ya kai ya kashe mutane tara a kasar, tare da bayyana hakan da cewa alamu ne na dawowar akidar wariya.

Ta ce dukkanin alamu suna nuni da cewa, a halin yanzu akwai masu dauke da akidar tsatsauran ra'ayi na kin jinin wasu jama'a wadanda ba jamusawa ba, ko kuma wadanda ba su da tsatsauran ra'ayi irin wannan,

A daren Laraba da ta gabata ce wani mutum dauke da bindiga ya bude wuta a wani wurin shan kahwa a garin Hanau, inda ya kashe mutane tara, daga bisani kuma aka samu gawarsa da gawar kakarsa  acikin gidansa, inda ake zaton cewa ya kashe kakarsa sannan ya kashe kansa.

Rahotanni sun ce an samu gawar wani musulmi bakurde daga cikin gawawwakin mutane tara da mutumin ya kashe a daren Larabar da ta gabata.

 

3880172

 

captcha