Wasu majiyoyi a kasar ta Turkiya sun nakalto daga shafin kammafanin dillancin labarai na reauters cewa, harin wanda aka kai a daren sabuwar shekarar miladiyya a wurin shakatawar da ke birnin Istanbul, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 39, yayin da wasu 69 kuam suka samu raunuka.
Abin tuni a na koa jiya ma wani dan bindigar ya sake kaddamar da wani hari da bindiga a kan masallacin Pasha da ke cikin birnin na Istanbul, inda ya jikka wasu mutane biyu a kalla.
Kasar Turkiya dai ta kasance a sahun gaba wajen daukar nauyin kungiyoyin 'yan ta'addan Daesh, wadanda a halin yanzu suka dawo a kanta.