IQNA

Ana Hankoron Gurfanar Da Sheikh Zakzaky A Najeriya

22:44 - December 06, 2016
Lambar Labari: 3481007
Bangaren kasa da kasa, Gwamnatin jihar Kaduna a tarayyar Nigeria ta fitta wani rahoto a yau Litinin wanda ya nuna cewa harka Islamiya ta Sheikh Ibrahim El-Zazzaky ta yan tawaye ne.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar PressTV cewa, gwamnatin ta fitar a yau Litinin yana cewa harka Islamia karkashin jagorancin Sheikh IbrahimYakun El-Zazzagi harka ce ta masu fada da gwamnati, kuma a haka gwamnatin zata dauke ta. Bayanin ya kara da cewa gwamnatin jihar Kaduna zata gurfanar da shugaban wannan harka kan dukkanin laifuffuka da kuma da kumasabawa dokokin kasa wanda yayan harkan suke yi.

Bayanin ya kara da cewa shugaban harkar Islamia ta yan shia yana da cikekken biyayye daga magoya bayansa don haka shi zai dauki nauyin dukkan abinda suka aikata na rashin biyayya da kuma sabawa doka.

Gwamnatin jihar ta kaduna ta fitar da wannan bayanin ne bayan da ta kammala nazarin rahoton komitin da ta kafa don binciken abubuwan da suka faru tsakanin sojoji da kuma mabiya harka Islamiya Islamic Movement in Nigeria IMN a cikin watan Decemban shekarar da ta gabata.

Dangane da hukunta sojojin da suke da hannu wajen kisan yan shia mabiya harka Islamia fiye da dari uku kuma, bayanin ya ce gwamnatin jihar ba zata yi kome a kai ba, don gwamnatin tarayyar ce zata kula da wannan bangaren .

Wadanbayanin ya fito ne kwanaki kadan bayan nasarar da Sheikh Ibrahim El-zazzgi ya samu kan karar da ya shigar a kotu kan gwamnatin tarayyar da kuma hukumar dss wacce take tsare da shi tun kimani shekara guda kenan.

3551688


captcha