IQNA

Binciken ISESCO Kan Makomar Duniyar Musulmi A Shekara Ta 2050

23:48 - February 19, 2020
Lambar Labari: 3484538
Tehran - (IQNA) cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasashen musulmi tana da shirin gudanar da wani bincike kan makomar duniyar musulmi a 2050

Salem Bin Muhammad Almalik babban sakaren cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasashen musulmi, ya bayyana cewa cibiyar tana da shirin gudanar da wani bincike kan makomar duniyar musulmi a 2050, ta kuma fara shirye-shirye kan hakan.

Kamfanin dillancin labaran yuna ya bayar da rahoton cewa, Salem bin Muhammad Almalik babban sakataren cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adun kasashen musulmi na duniya ya bayyana cewa, suna da kyakkyawan shiruin da gudanar da bincike kan yadda ake hasashen makomar duniyar musulmi.

Ya ce wannan hasashe zai kama daga shekarar da aka shiga har zuwa shekara ta 2050, wato kimanin shekaru talatin masu zuwa, wanda hakan zai hada mahangar masana kan lamurran suke kai da komowa, dada sassa na duniya.

Bin Muhammad ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a taron farko na kwanaki biyu da aka shirya kan hakan.

Ya kuma jaddada cewa babban abin fata shi ne a samu gagarumin ci gaba a cikin harkokin kasashen musulmi a cikin wadannan shekaru musamman ma ta fuskar bunkasar ilimi da kere-kere da kuma samar da ayyukan yi, wanda kuma za a kara tattauna wanann batun a zaman da kungiyar za ta gudanar a cikin watan Yuli 2020.

 

 

 

3879932

 

Abubuwan Da Ya Shafa: isesco
captcha