IQNA

ISESCO: Shekarar 2019 Shekara Ce Ta Bunkasa A’adu Da Koyarwar Musulunci

23:48 - December 31, 2018
Lambar Labari: 3483268
Bangaren kasa da kasa, hukumar bunkasa al’adu ta kasashen musulmi ISESCO ta ce shekarar 2019 za ta zama shekarar zage dantse domin yada koyarwar musulunci a duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin bayanin da hukumar ta ISESCO ta fitar ta bayyanacewa, muuslmi za su yi amfani da wannan damar a cikin wannan shekara domin mayar da hankali ga wannan gagarumin aiki.

Bayanin ya ci gaba da cewa, bisa la’akari da yadda aka bata sunan muslucnia  cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan ga wasu al’ummomi wadanda ba musulmi, ya zama wajibi kan musulmin da su mike domin nuna wa duniya cewa addinin muslunci bas hi ne abin da su suka dauka ba.

Dole ne masana daga cikin musulmi da malamai su bayar da dukkanin gudunmawarsu wajen cimma wannan manufa ta isar da sahihin tunani da mahanga ta musulunci, wadda ta ginua  kan girmama dan adam da mutunta shi, da girmama addininsa da mahangarsa.

Kamar yadda kuma bisa koyarwar musulunci babu tashin hankali, bil hasali ma kaida cea cikin addinin muslucni cewa babu tilasci a cikin addini, saboda haka musulunci baya muzgunawa wani saboda shi ba musulmi ba ne.

3777406

 

captcha