IQNA

ISESCO Ta Yi Allahawa Wadai Da Kisan ‘Yan Shi’a A Kasar Saudiyyah

21:56 - October 18, 2015
Lambar Labari: 3388694
Bangaren kasa da kasa, kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adu ta kasashen musulmi ta yi Allawadai da kakkasar murya dangane da harin da aka kai kan Husainiyar Haidariyya ta mabiya mazhabar shi’a a yankin Saihat na gabacin saudiyya.


Kamfanin dilalncin labaran iqna yahabarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na isesco.org.ma cewa, kungiyar ta ISESCO ta yi Allawadai da kakkasar murya dangane da harin da aka kai kan Husainiyar Haidariyya ta mabiya mazhabar shi’a a yankin Saihat na gabacin Saudiyya a cikin wannan mako.



Wannan aiki na ta’addanci da ya yi sanadiyyar yin shahadar wasu daga cikin ‘yan kasar dalili na zahiri da ke kara tabbatar da cewa Daesh kungiyar ce ta ‘yan ta’adda da suke da karkataccen tunani.



Bayanin kungiyar ya ce abin da wadannan mutane suke aikatawa, shi ne bayyana abin ayar da ke magana kan masu barna a bayan kasa (Mufsidin) wadanda ba su mutunta darajar abu mai daraja sun keta hurumin masallata da wuraren ibada na muslmi.

3388338

Abubuwan Da Ya Shafa: isesco
captcha