Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, cibiyar koyar da kur'ani ta kasa da kasa ta Astan Muqaddas Hosseini ta reshenta na kasar Indonesia ta gudanar da gasar haddar kur'ani mai tsarki a shekara ta shida a jere a birnin Jakarta.
Abdullah Beyk shugaban cibiyar reshen birnin Jakarta ya bayyana cewa: A daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan maulidin manzon Allah (SAW), wanda ake ci gaba da gudanar da bukukuwan na tsawon wata guda a garuruwa daban-daban na kasar Indonesia, reshen cibiyar yada alkur'ani ta Astan Hosseini. sun shirya wata gasa ta musamman na haddar kur'ani mai tsarki
Ya kara da cewa: Sama da mahalarta 200 maza da mata ne suka halarci wannan gasa wadda aka gudanar a ginin reshen cibiyar koyar da kur’ani ta Astan Hosseini da ke Jakarta, kuma daga karshe an bayar da kyautuka ga wadanda suka yi nasara.
Al-Habib Hossein bin Hamid al-Attas, malamin kur’ani, ya jaddada wajabcin riko da kur’ani da sunna, sannan ya godewa iyayen daliban da suka halarci wannan taro kan yadda suke taimaka wa ‘ya’yansu wajen shiryawa da karfafa musu gwiwa wajen shiga shirye-shiryen kur’ani.