IQNA

Kyawawan karatun ma'aikacin agaji na Falasdinu

15:45 - October 15, 2023
Lambar Labari: 3489981
Gaza (IQNA) Kyakkyawan karatun ma'aikacin agaji na Falasdinu daga Gaza ya samu karbuwa sosai daga masu amfani da shafukan sada zumunta.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yeni Shafaq cewa, an lura da kyakykyawan karatun ma’aikacin agajin Palastinu daga zirin Gaza daga aya ta 153 zuwa 155 a cikin suratul Baqarah sakamakon kyakykyawan sauti da ma’anar wadannan ayoyi daga masu amfani da yanar gizo.

Kafofin yada labaran Falasdinu sun bayar da rahoton cewa, adadin shahidan Palasdinawa ya karu zuwa fiye da 2,200, yayin da adadin wadanda suka jikkata ya karu zuwa sama da 8,000 tun bayan da yahudawan sahyuniya suka fara kai farmaki a zirin Gaza.

Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta hana shigar da kayan agaji zuwa zirin Gaza tare da neman mazauna yankin arewacin kasar da su fice daga yankin, matakin da wasu da dama ke kallonsa a matsayin laifin yaki.

 

4175337

 

Abubuwan Da Ya Shafa: laifi jikkata falastinawa Baqarah aya
captcha