Kafofin yada labaran kasar faransa sun bayar da rahotannin cewa, Majalisar dokokin kasar ta amince da wani kudirin doka mai cike da cece-kuce duk da kakkausar suka daga bangaren ‘yan majalisun jam’iyyun adawa.
Gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ta yi ikirarin cewa ana bukatar dokar ne domin karfafa tsarin gudanar da addini a Faransa, to sai dai masu suka na cewa matakin keta ‘yancin addini ne.
Bayan muhawara ta tsawon watanni bakwai da akayi ta kai ruwa rana tsakanin bangarorin siyasar kasar, daga karshe ‘yan majalisa su arba’in da tara suka amince da dokar yayin da sha tara suka ki amincewa, sai kuma wasu biyar sukayi rowan kuri’unsu.