IQNA

Hizbullah: Manufar Harin Amurka Kan Dakarun Hashd Al-shaabi Ita Ce Raunana Iraki Da Syria

23:52 - June 28, 2021
Lambar Labari: 3486058
Tehran (IQNA) Kungiyar Hizbullah ta bayyana harin da Amurka ta kai kan sansanonin dakarun Hashd Al-shaabi a daren jiya da cewa, yunkuri ne na neman raunana Iraki da Syria.

A cikin wani bayani da ta fitar a yau, kungiyar Hizbullah ta yi Allawadai da hare-haren Amurka kan sansanonin dakarun sa-kai na al'ummar kasar Iraki, wato Hashd Al-shaabi a kan iyakokin Iraki da Syria.

Bayanin na kungiyar Hizbulah ya ce, wadannan hare-haren na Amurka a cikin wadanann kasashe biyu, ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na kasa da kasa, wanda Amurka ta cancanci a hukunta kan hakan.

Baya ga haka kuma, Hizbullah ta jinjina wa gwamnatin Iraki da kuma al'ummar kasar baki daya, da suka nuna rashina mincewarsu da hakan, tare da yin Allawadai da Amurka, da kuma neman a dauki matakin da ya dace wajen tunkarar irin wannan shishigi na Amurka da wuce gona da iri.

Fadar White House ta sanar da cewa jiragen Amurka sun kai harin ne bisa umarnin shugaban kasar, bisa hujjar cewa wadanda aka kai wa harin suna mara baya ne ga Iran, kuma suna amfani da sansanoninsu wajen kai wa sojojin Amurka hare-hare da jiragen yaki marasa matuki.

Tuni gwamnatin Iraki ta fitar da bayani na rashin amincewa da hakan, tare da bayyana cewa ba yarda da irin wannan aikin na Amurka a cikin kasarta ba, saboda haka za ta dauki matakin da ya dace.

Su a nasu bangaren dakarun Hashd Al-shaabi sun ce Amurka ta kwana da shiri, domin kuwa martani yana nan tafe, domin daukar fansa kan dakaru hudu da suka rasa rayukansu a harin na Amurka.

 

 

 

3980727

 

captcha