IQNA

Mauritaniya Ta Lashe Gasar Kiran Sallah Ta Kasashen Yammacin Afirka

23:04 - May 25, 2021
Lambar Labari: 3485949
Tehran (IQNA) Muhammad Abdul Ja dan kasar Mauritaniya ya lashe gasar kiran sallah ta kasashen yammacin nahiyar Afirka.

Kamfanin dillancin labaran Al-akhbar na kasar Mauritaniya ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da wannan gasa ne da taken Bilal Bin Rabah Allah ya kara masa yarda, wanda sahabin manzon Allah (SAW) ne kuma ladani na farko a tarihin addinin muslunci.

Gasar ta gudana nea  birnin Dakar an kasar Senegal, inda wakilai daga kasashen yammacin nahiyar Afirka suka halarta, amma matashi dan kasar Mauritaniya Muhammad Abdul Ja shi ne ya lashe gasar.

Matashin mai shekaru 12 da haihuwa, ya samu kyautuka bayan kammala gasar, kamar yadda kuma ya samu tarbe bayan komarwasa gida a jiya Litinin.

3973628

 

 

captcha