IQNA

Tarukan Muharram A Cikin Kwararan Matakai A Najaf

23:38 - August 21, 2020
Lambar Labari: 3485107
Tehran (IQNA) sakamakon yanayin da ake cikin an sanar da cewa za a gudanar da tarukan Muharram a Najaf a cikin kwararan matakai.

Bangaren yada labarai na hubbaren Alawi a Najaf na kasar Iraki ya sanar da cewa, sakamakon yanayin da ake cikin an sanar da cewa za a gudanar da tarukan Muharram a birnin a cikin kwararan matakai na kiwon lafiya bisa umarnin babban malamin addini na kasar Ayatollah Sayyid Ali Sistani.

Faiq Al-shommari daya daga cikin mambobin kwamitin kula da hubbaren ya bayyana cewa, daukar wannan mataki ya zama wajibi, bisa la’akari da yaduwar cutar corona da ake samu, musamman ma kuma ganin cewa wadannan taruka ne da ke tara jama’a masu yawa.

Ya kara da cewa, daga cikin matakan da za a dauka, baya ga wadanda suka shafi daidaikun mutane, kamar bayar da tazara da kuma saka takunkumin fuska da amfani da sanadaren kashe kwayoyin cuta, za a dauki matakai na rage yawan adadin mutanen da za su halarci wurin.

 

3917966

 

 

captcha