IQNA

Daya Daga Cikin Malaman Iraki ya Bayani kan tarukan Muharram Na Bana

14:48 - August 19, 2020
1
Lambar Labari: 3485102
Tehran (IQNA) Ayatollah Muhammad Taqi Mudarris ya kirayi al’ummar Iraki da su zauna gida a lokutan juyayi na muharram.

Kamfanin dillancin labaran Saumaria News na Iraki ya bayar da rahoton cewa, daya daga cikin amnyan malaman addini na kasar Iraki  Ayatollah Muhammad Taqi Mudarris ya kirayi al’ummar Iraki da su zauna gida a lokutan juyayi na muharram saboda yanayin da ake ciki.

Malamin ya ce za a iya mayar gidaje wurin taruka da adadi kadan na mahalrta domin raya ranaku na juyayi, amma babu bukatar gudanar da manyan taruka a hubbarori.

Ya ce yin hakan ba gazawa ba ce, hakan ma wata jarunta c eta musamman, kare lafiyar kai da kuma kare lafiyar sauran jama’a.

Malaman mabiya mazhabar ahlul bait a kasashen Lebanon, Bahrain, Iraki da Ingila da ma wasu kasashe duk sun dauki irin wadannan matakai.

 

3917465

 

 

 

 

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
auwal muhd
0
0
hakan yayi daidai a zauna ayi a gida
captcha