Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Musatafa Madbuli fira ministan kasar Masar ya bayyana cewa, a babbar salla kamar karamar salla da ta gaba ne. za ayi sallar idi a masallaci daya ne.
Ya ce bisa la'akari da halin da ake ciki na yaduwar cutar corona, dole nea ci gaba da daukar matakan da suka dace domin dakile yaduwar cutar a tsakanin jama'a.
Kamar yadda ya jadda cewa hatta a inda za a gudanar da sallar, za a dauki matakan da suka dace na kiyaye kaidoji kiwon lafiya.
A halin yanzu dai a kasar Masar akwai mutane 91,583 da suka kamu, yayin da 4,558 suka rasa rayukansu.