IQNA

Majami’oin Kirista Na Duniya Sun Bukaci Tarayyar Turai Ta Dauki Mataki Kan Isra’ila

23:46 - May 13, 2020
Lambar Labari: 3484793
Tehran (IQNA)  majami’oin mabiya addinin kirista sun bukaci tarayyar turai da ta taka wa Isra’ila burki kan shirinta na mamaye yankunan Falastinawa.

A cikin wasiku guda biyu na hadin gwiwa da Majalisar majami’oin mabiya addinin kirista ta duniya, da kuma majalisar majami’oin kiristocin gabas ta tsakiya, suka aike wa kungiyar tarayyar turai, sun bukaci kungiyar da ta gudanar da bincike kan shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa na gabar yadda da kogin Jordan, tare da daukar matakai na hana faruwar hakan.

Bayanin majami’oin mabiya addinin kiristan ya ce, wannan mataki da Isra’ila take shirin dauka zalunci ne, wanda bai kamata al’ummomin duniya su yi shiru a kansa ba, kuam hakan babu abin da zai kawo in banda karin tashin hankali a yankin, kamar yadda kuma wannan mataki ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na kasa da kasa.

Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da cewa, idan har kungiyar tarayyar turai ba ta dauki wani mataki kan hakan ba, to majalisar majami’oin mabiya addinin kirista za ta dauki hakan a matsayin hadin baki tsakaninsu da Isra’ila.

 

3898321

 

 

 

 

 

captcha