IQNA

An Rusa Cibiyar Da’awa Islamiyya A Kasar Sudan

23:57 - April 11, 2020
Lambar Labari: 3484701
Tehran (IQNA) an rusa babbar cibiyar nan ta da’awa Islamiyya mai gudanar da ayyukan jin kai a kasar Sudan.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a yau  mahukuntan kasar Sudan sun sanar da rusa cibiyar da’awa a kasar, tare da kwace dukkanin kaddarori mallakin cibiyar da kuma na jagororinta.

Wujdi Saleh daya daga cikin mambobin hukumar da yaki da mallakar kaddarorin haram ta kasar Sudan ya bayyana cewa, an rusa wannan cibiya tare da haramta dukkanin ayyukanta a cikin kasar Sudan, da kuma haramta kaddarorinta.

Shugaban majalisar kolin gudanarwa ta kasar Sudan Abdulfattah Burhan ya bayar da umanin kwace dukkanin kaddarorin cibiyar a cikin kwanaki, tare da mayar da su  a cikin baitul mali na gwamnatin kasar.

An kafa wannan cibiya tun a cikin shekara ta 1980 a birnin Khartum, kuma cibiya ce mai zaman kanta wadda ba ta da alaka da gwamnati, wadda take gudanar da ayyukan jin kai ga talakawa marassa galihu, kuma tana da ofisoshia kasahe 40 na Afrika da suke gudanar da irin wannan aiki.

3890710

 

 

captcha