IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Kur’ani Ta Kasa A Najeriya

23:40 - December 30, 2018
Lambar Labari: 3483264
Bangaren kasa  da kasa, an fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya a Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jaridar Daily Trust cewa, an fara gudanar da gasar karo na 33 ne a garin Gombe fadar mulkin jahar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Ibrahim Hassan Dan Kwambo gwamnan jahar ta Gombe shi ne ya jagoranci bude taron gasar, inda ya bayyana cewa, gasar kur’ani mai tsarki tana daya dagacikin abin da yake hada kan al’ummar kasa.

Abdullahi Abu Zuru daga jami’ar Dan Fodio kuma daya daga cikin wadanda suka shirya gasar, ya bayyana cewa duk da cewa wannan shi ne karo na 33 da ake gudanar da gasar, amma akwai gagarumin ci gaba da aka samu a bangarori daban-daban na gasar.

Daga ciki kuwa har da yadda a halin yanzu a bangarori shida ne ake gudanar da ita, wanda ada a bangaren karatu da kuma harda ne kawai, inda yanzu an kara da ilmomin tajwidi da kuma tafsiri da ma wasu bangarorin na ilimin kur’ani mai tsarki.

3776800

 

captcha