IQNA

An Kai Wani Harin Ta’addanci A Birnin Iskandariya Na Masar

23:21 - March 25, 2018
Lambar Labari: 3482510
Bangaren kasa da kasa, an kai ani harin ta’addanci a birnin Ikandariya na kasar Masar wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkatar mutane.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an kai harin ne da wata mota da aka shakare da bama-bamai a yakin Romani da ke cikin birnin iskandariya a jiya Asaba, kuma mutane hudu ne suka mutu.

Wadanda suka sheda lamarin da idanunsu sun bayyana cewa, harin ya nufi babban daraktan ma’aikatar tsaro ta lardin ne, amma ya tsallake rijiya ta baya.

A cikin ‘yan lokutan nan kasar Masar na fuskantar munanan hare-haren ta’addanci da ke lakume rayukan mutane da dama da suka hada da jami’an tsaro.

Kasar Masar dai na daga cikin kasashen larabawa da suka mika wuya ga matsin lamabar yahudawa da kuam ‘yan koransu na yankin, domin taimaka musu wajen cimma manufofinsu a yankin gabas ta tsakiya.

3701864

 

 

 

 

captcha