IQNA

Fushin Amurka A Kan Daftarin Kudirin Kwamitin Tsaro Kan Quds

21:14 - December 19, 2017
Lambar Labari: 3482216
Bangaren kasa da kasa, Amurka ta nuna fushinta matuka dangane da daftarin kudirin da kasashen larabawa suka gabatar a gaban kwamitin tsaro kan batun birnin Quds.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Kasar Amurka ta hau kujeran naki dangane da wani kuduri da Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya so fitarwa a daren jiya da nufin kiran gwamnatin Amurka da ta janye matsayar da ta dauka na bayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Rahotanni sun bayyana cewar a zaman da kwamitin tsaron ya gabatar a daren jiya don tattaunawa kan wani daftarin kuduri da kasar Masar ta gabatar wa kwamitin kan birnin na Kudus, Amurka ta hau kujerar naki kan daftarin kuduri a daidai lokacin da ake kada kuri'ar amincewa ko rashin amincewa da shi.

A ranar Asabar din da ta gabata ce kasar Masar ta gabatar da daftarin kudurin inda kasashe 14 daga cikin 15 membobin Kwamitin Tsaron suka amince da shi, in ban da Amurka wacce ta yi amfani da karfin hawa kujerar naki da take da shi, ta yi watsi da daftarin kudurin.

A bisa kudurin Kwamitin Tsaron mai lamba dari hudu da sabain da bakwai, an bukaci dukkanin kasashen duniya da su guji kafa duk wata cibiya ta diplomasiyya a birnin na Kudus, wanda matsayar da gwamnatin Amurka ta dauka yana nuni da karen tsayen da take yi wa dokokin kasa da kasa ne.

3674131

 

 

 

captcha