IQNA

Daesh Ta Tabbatar da Mutuwar Jagoranta Albaghdadi

21:57 - July 11, 2017
Lambar Labari: 3481689
Bangaren kasa da kasa, Cikin Sanarwar da fitar, Kungiyar Ta'adancin Ta ISIS ta tabbatar da mutuwar Shugaban ta Abubakar Bagdadi
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, kamfanin dilalncin labaran Saumaria News daga Iraki ya bayar da rahoton cewa, a wannan Talata Kungiyar ta'addanci ta ISIS ta fitar da wani kajeran labari inda a cikin sa ta tabbatar da mutuwar Shugabanta Abubakar Bagadadi tare da cewa nan gaba za ta sanar da sabon Khalifanta.

Kafar watsa labaran ta ce kwanaki biyu da suka gabata, cikin wani sako da fitar a shafinta na Intagram kungiyar ta ISIS ta haramta watsa duk wani labari da ya shafi mutuwar Shugaban Kungiyar Abubakar Bagdadi, domin hakan ne ma masu sharhi ke ganin cewa wannan shi ne dalilin da ya sanya kungiyar ta ISIS ta gaggauta tabbatar da mutuwar ta Bagdadi.

Tun ranar sha shiga ga watan Yuni da ya gabata rasha ta sanar da cewa ta halaka shi a kusa da garin Raqqah, a yau kuma kungiyar 'yan ta'addan ta ISIS ta tabbatar da halakar tasa.

3617760


captcha