IQNA

Dalibai Musulmi Sun Samar Da Shiri Mai Taken Monologue A Amurka

23:02 - April 05, 2017
Lambar Labari: 3481378
Bangaren kasa da kasa, daliban jami’ar Michigan musulmi sun samar da wani shiri mai taken monologue da nufin wayar da kan sauran dalibai kan addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani ma iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Michigan Daily ya bayar da rahoton cewa an samar da wannan shiri ne domin fito da sautin musulmi da ba a ji.

Bayanin ya ci gaba da cewa dalibai 10 ne suka kirkiro wannan shiri inda suke taruwa a bababn dakin taruka tare da gayyatar sauran dalibai musulmi da kuma wadanda ba msuulmi ba, inda suke gabatar da shirye-shirye masu kayatarwa na wayar da kai kan musulunci.

Daga muhimman abubuwan da shirin ke mayar da hankalia kansa shi ne fito da hakikanin kyakkyawar koyarwa irin ta addinin muslunci, sabanin abin da ake yadawa mutane a kansa wand aba gaskiya ba ne.

Daga ciki kuwa har da rera wakoki na musamman ta hanyoyi na zamani, inda a ciki ake bayanin muslunci da kuma koyarwarsa da yadda yake girmama dan adam da kuma girmama sauran addinai, da kira zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin bil adama.

Misha Sheikh daya daga cikin daliban jami’ar Michigan da ta gama karatu, tana daga cikin wadanda suka kirkiro wannan shiri, ta kma bayyana cewa hakika akwai babbar matsala a kan yadda mutane da dama suke kallon addinin muslunci.

Kuma wajibi ne a kansu su mike domin wayar da kan jama’a dangane da muslunci, su nna ma mutane koyar muslunci ta gaskiya.

3587063

captcha