IQNA

Independent Ta Buga Makala Da Ke Sukar Dokar Hana Saka Lullubi A Turai

22:52 - March 17, 2017
Lambar Labari: 3481321
Bangaren kasa da kasa, Jaridar Independent ta kasar Birtaniya, kuma daya daga cikin manyan jaridu na nahiyar turai, ta buga wata makala da ke yin kakkausar suka dangane da okar hana mata musulmi saka lullubi a wuraren aikinsu a cikin kasashen anhiyar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, wannan makalar wadda wata marubuci mai suna Sofia Ahmad ta rubuta, ta mayar da hankali ne kan yadda wannan hukunci na babbar kotun kungiyar tarayyar turai ya yi hannun riga da dokokin kungiyar.

Sofia Ahmad wadda fitaciyar marubuciya a kasar Birtaniya ta bayyana cewa, tsarin kungiyar tarayyar turai bai ginu a kan addini ba, amma ya ginu a kan girmama dukkanin addinai da baiwa kowa hakkinsa na addini ko akida.

Ta ce wannan hukunci da kotun kolin tarayyar turai yanke kan cewa kamfanoni suna da hakkin su hana mata musulmi saka lullubi a wurin aiki, ya yi hannun riga da wannan ka'ida ta kungiyar tarayyar, kuma yin hakan ya saka kungiyar a cikin bakin tarihi na tauye hakkokin addinai a hukumance.

Daga karshe ta ce idan kotun tarayyar turai ta fake da batun ta'addanci ta yanke hukunci a kan dukkanin musulmi, shi ma wannan ba adalci ba ne da aka san shari'a da shi, domin kuwa kotun tarayyar turai ko su wane ne 'yan ta'adda, ta san kasashen da suka kirkiro su kuma suke daukar nauyinsu, amma saboda mashalar da ke tsakanin kasashen turai da kasashen da ke daukar nauyin 'yan ta'adda kotu ba ta bijiro da wannan batun ba.

3584624

captcha