Mahukuntan suka ce asalin garin Mangdo na mabiya addinin Buda ne, amma daga bisani 'yan kabilar Rohingya da suka shigo cikin kasar daga Bangadasha suka zauna wurin, a kan haka mabiya addinin Buda za su dawo wurinsu, yayin da muuslmin da ke wurin za a mayar da su zuwa kauyukan da aka gina musua wasu wuraren na daban.
Fiye da kashi 98 na mutanen da suke zaune a wannan gari dai mabiya addinin muslunci ne 'yan kabilar Rohingya, yayin da adadin masu bin addinin Buda a garin bai wuce kashi 2 cikin dari ba, kuma muuslmi suna zaune da su lafiya tsawon daruruwan shekaru ba a taba jin tsakaninsu.
Kimanin watanni da suka gabata ne dai jami'an tsaron gwamnatin Myanmar suka yi wa musulmi kisan gilla a wannan yanki, tare da kone musu gidaje da kaddarori.