IQNA

Za A Gina Sabon Masallaci Yankin Welta Na Kasar Ghana

23:43 - August 24, 2016
Lambar Labari: 3480740
Bangaren kasa da kasa, za a gina wani sabon masallaci a yankin Welta da ke yammacin kasar Ghana.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yanar gizo na Ghana web cewa, cibiyar bayar da agaji da Hilal Ahmar ta kasar UAE ce za ta dauki nauyin gina wannan masalalci.

Wannan cibiyar ta kasar hadaddiyar daular latrabawa ta dauki nauyin gina wannan katafaren masalalci, kamar yadda kuma ta bayyana cewa tana shirin gina makamancinsa a yankin arewacin kasar, wanda akasarinsa maboya addinin muslunci ne.

Kasar Ghana dai tana daga cikin muhimman kasashen yammacin nahiyar Afirka, kuma tana tafiya ne a akn tsari na jamhuriya wadda jam’iyyun daban-daban suke tafiyarwa.

Mabiya addinin kirista dais u ne suka yawa a cikin al’ummar kasar Ghana, kamar yadda kuma baya ga addinin kiristanci sai addinin muslnci, sai kuma addinai na gargajiya, wadanda tun asali mutanen kasar suke binsu kafin su karbi kiristanci da muslunci.

3525146

captcha