IQNA

Wayar Da Kasan Dalibai Kiristoci Dangane Da Musulunci A Zimbabwe

23:52 - August 08, 2016
Lambar Labari: 3480691
Bangaren kasa da kasa, karamin ofishin jakadancin kasar Iran a Zimbabwe ya shirya taron wayar da kai ga dalibai kan addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran Kur’ani na Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al’adun muslunci cewa, wannan kasa wadda akasarin mutanen kiristoci kamar wasu sauran kasashen kasashen Afirka, ana samun matsalar kyamar musulmi, saboda ayyuka na ta’addanci da wasu kungiyoyi suke aikatawa kamar Boko Haram.

Karamin ofishin jakadancin Iran ya shirya wannan karamin taron na wayar da kan dalibai kiristoci dangane da addinin muslunci a masalalci Ali Muhammad da ke birnin Harare fadar mulkin kasar.

Daya daga cikin malaman kasar Iran Mahdawi shi ne ya jagoranci wanann wannan taro, inda aka koyar da su abubuwa da dama suka danganci muslunci domin su san yadda suke, maimakon yadda ake gaya musu daga bakin wadanda ba musulmi ba.

Daga cikina bubuwan da aka koyar da su akwai matsayin abinci a muslunci, da kumayadda muslunci ya dauki Maryam (SA) da kuma annabi Isa (AS) wadanda suna da matsayi na kololuwa acikin addinin muslunci, kamar yadda kur’ani ya koyar da musulmi hakan.

Taron ya samu halartar wakilai daga makarantu na Zivara da sahkuwa, Lord Malon, Alles Robins da sauransu, inda aka samu halaetar daruruwan dalibai da ska halarci taron tare da nuna farin ciki da gamsuwa da abin da suka ji.

3521212


Wayar Da Kasan Dalibai Kiristoci Dangane Da Musulunci A Zimbabwe

Wayar Da Kasan Dalibai Kiristoci Dangane Da Musulunci A Zimbabwe


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna%2c
captcha