IQNA

Yaro Dan Shekaru 3 Ya Hardace Dukkanin Kur'ani A Najeriya

23:52 - August 07, 2016
Lambar Labari: 3480685
Bangaren kasa da kasa, wani mai matukar ban mamaki shi ne yadda aka samu wani karamin yaro mai karancin shekaru da ya hardace kur'ani a garin Zaria da ke Najeriya.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar Uyun Khalij cewa, jaridar Daily Trust ta bayar da rahoton cewa, wannan yaro yan ada karfin kwakwalwa, kuma ya samu nasarar hardace kur'ani tare da halartar gasar kur'ani a garin na Zaria.

Rahoton ya ce wannan yaro mai suna Muhammad Shamsuddin Ali ya kasance ana halartar makarantar kur'ani da shi ta Sheikh Anju Ango Abdullahi yana da shekara guda da rabi, amma lokacin da ya cika shekaru ya kammala hardace kur'ani baki daya.

Ali Shasuddini shi ne mahaifin wannan yaro, ya kuma bayyana cewa bai taba tsammanin cewa haka dansa yake ba, Allah yaba shi kwalwa mai saurin dauka da rikewa, wanda hakan babban abin fahari ne gare shi da dukkanin al'ummar musulmi baki daya.

Haka nan kuma wannan karamin yaro ya kasance yana Magana da harsunan larabci da kuma turancin ingilishi.

Birnin zaria dai ya kasance birnin mai matukar muhimmanci ga mabiya tafarkin iyalan gidan manzo da suke gudanar da tarukansu.

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna%2c
captcha