IQNA

Sabon Shirin Na Yanar Gizo Kan Sanin Mazhabar Iyalan Gidan Manzo

12:09 - July 28, 2012
Lambar Labari: 2378907
Bnagaren kur’ani, a taron baje kolin kur’ani mai tsarki na kasa da kasa da ke gudana a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci an nuna wani sabon shiri na yanar gizo da ke aiki da na’ura mai kwakwalwa kan ilimin sanin mazhabar iyalan gidan manzon Allah.

Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa cewa a taron baje kolin kur’ani mai tsarki na kasa da kasa da ke gudana a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci an nuna wani sabon shiri na yanar gizo da ke aiki da na’ura mai kwakwalwa kan ilimin sanin mazhabar iyalan gidan manzon Allah, tisa da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyakan gidansa tsarkaka.
Bayanin ya ci gaba da cewa bababr manufar fitar da wannan shiri dai it ace, kara saukaka hanyoyin bincike ga masu nazari da bincike a jami’oi ko kuma marubuta wadanda suke samun masaniya kan lamurra da dama da suka danganci mazhabar iyalan gidan manzon Allah, inda aka hada muhimman lamurra na ilimi da suka danganci wannan mazhaba a cikin sauki ta yadda mai bincike zai gudanar da aikinsa ba tare da gajiya ba.
Jiya a wurin taron baje kolin kur’ani mai tsarki na kasa da kasa da ke gudana a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci an nuna wani sabon shiri na yanar gizo da ke aiki da na’ura mai kwakwalwa kan ilimin sanin mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garshe da iyalansa.
1063614

captcha