IQNA

Makaranta Da Mahardata Kur’ani 77 Daga Masar Na Ziyara A Kasar Iran

11:55 - July 22, 2012
Lambar Labari: 2374434
Bangaren kur’ani, makaranta da mahardata kur’ani mai tsarki daga kasar Masar 77 ne yanzu haka suke gudanar da ziyara a kasar Iran domin halartar wurare na karatu da gasarv kur’ani da ake gudanarwa acikin wannan wata mai alfarma tare da yin rangadia wuraren da ake gudanar da taruka na baje kolin kayayyakin kur’ani mai tsarki a garuruwan kasar musamman baje kolin kur’ani na duniya a karo na ashirin.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, yanzu haka makaranta da mahardata kur’ani mai tsarki daga kasar Masar 77 ne suke gudanar da ziyara a kasar Iran domin halartar wurare na karatu da gasarv kur’ani da ake gudanarwa acikin wannan wata mai alfarma tare da yin rangadia wuraren da ake gudanar da taruka na baje kolin kayayyakin kur’ani mai tsarki a garuruwan kasar musamman baje kolin kur’ani na duniya a karo na ashirin a birnin Tehran.
A daren yau ne za a gudanar da wani shiri na karatun kur’ani mai tsarki wanda aka baiwa take taurarin sama wanda zai samu halartar makaranta kur’ani mai tsarki da kuma mahardata da suka hada har da masu halartar gasar duniya domin su shiga cikin wannan shiri mai albarka kamar dai yadda aka saba gudanar da tarukan makamantan haka a lokutan azumin watan Ramadan.
Tun tsawon shekaru ashirin da suka gabata ne aka fara gudanar da taron baje kolin kur’ani mai tsarki na kasa da kasa abirnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci, wanda shi ne irinsa na farko da ke samun halartar wasu cibiyoyi na kur’ani daga kasashen musulmi da na larabawa kamar dai yadda masu shirya taron suka bayyana, inda ake nunawa har ma da sayar da abubuwan da aka baje a wurin na baje koli.
1058435

captcha