IQNA

Kimanin Makaranta Da Mahardata 80 Ne Suka Yi Rangad A Dakunan Watsa Shirin Kur’ani

11:56 - July 22, 2012
Lambar Labari: 2374421
Bangaren kur’ani, kimanin makaranta da mahardata 80 daga kasar Masar suka yi rangadi a wasu dakunan watsa shirin radio da ya danganci kur’ani mai tsarki a wani shiri da ak atsara na kai makaranta duba sabon gidan radiyon kur’ani da zai rika watsa shirye-shiryensa acikin harsuna daban-daban.
Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa a Tehran cewa, a jiya kimanin makaranta da mahardata 80 daga kasar Masar suka yi rangadi a wasu dakunan watsa shirin radio da ya danganci kur’ani mai tsarki a wani shiri da ak atsara na kai makaranta duba sabon gidan radiyon kur’ani da zai rika watsa shirye-shiryensa acikin harsuna daban-daban da suke da karbuwa da yawan masu Magana da su musamman a cikin kasashen musulmi.
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewar ci gaban al'ummar musulmi da wayewarsu sun samo asali ne daga koyarwar alkur'ani da kyawawan dabi'un Musulunci, a jawabin da ya gabatar a gaban taron makaranta da mahaddata da kuma malamai a fannin ilimin alkur'ani mai girma da suka ziyarce shi a yau asabar; Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Uzma Sayyid Ali Khamene'i ya jaddada cewar shaharar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi ya samo asali ne daga dogaronta da Allah karkashin koyarwar alkur'ani mai girma.
Sannan yayi nuni kan sakamakon da mutum zai samu idan ya dogara da wayewa irin ta kasashen yammaci da ta ginu akan kawar duniya da nisantar kyawawan dabi'u yana mai jaddada cewa; babban misali kan da'awar karya da kasashen yammaci ke yi dangane da kare hakkin bil-Adama shi ne yin shiru kan kisan gillar da ake yi wa dubban musulmai a kasar Myanmar "Bama".
Jagoran ya kuma kara da cewa; wayewar yammaci tun a tsawon daruruwan shekaru da suka gabata har ya zuwa yanzu duk inda suka sanya kafa babu abin da zai bulla sai barna da bautar da dan Adam ta hanyar tatsarsa. Don haka Jagoran juyin juya halin Musulunci ya fayyace cewar ta hanyar aiki da koyarwar alkur'ani ne kadai za a kai ga samun daukaka, amincin rayuwa, jin dadi na zahiri da badini, kyawawan dabi'u da samun nasara kan makiya.
1058191
captcha