IQNA

Ana Kokarin Ganin An Kirayi Yan Majalisar Dokokin Malazia Zuwa Gasar Kur'ani

13:37 - July 16, 2012
Lambar Labari: 2369892
Bangaren kur'ani, masu kula da shirya tarukan gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Malazia sun sanar cewa suna kokarin ganin sun saka wani tsari da zai rika gayyatar yan majalisar dokokin kasar zuwa taruka na gasar karatun kur'ani mai tsarki a matsayi na kasa da kasa da ake gudanarwa kowace shekara a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na labaran yankin Asia cewa masu kula da shirya tarukan gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Malazia sun sanar cewa suna kokarin ganin sun saka wani tsari da zai rika gayyatar yan majalisar dokokin kasar zuwa taruka na gasar karatun kur'ani mai tsarki a matsayi na kasa da kasa da ake gudanarwa kowace shekara a kasar da ke gabacin duniya.
To a bangare guda kuma daruruwan 'ya kabilar kurdawa ne suka yi bata kashi tsakaninsu da 'yan sandan gwamnatin Turkiya a lokacin da suke gudanar da zanga-zanga a garin Diyar Bakar, domin neman a saki jagoran kungiyar Abdallah an da ake tsare da shi tun tsawon shekaru kimanin ashirin.
Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan sandan gwamnatin Turkiya sun fada kan kurdawa fararen hula masu zanga-zanga a garin na Diyar Bakar, inda suka yi da dukarsu da kulake da kuma watsa musu ruwan zafi da hayaki mai sanya hawaye, lamarin da yayi sanadiyar jikkatar da dama daga cikinsu, daga ciki kuwa hard a wani dan majalisar dokokin kasar daga bangaren adawa da a shiga cikin zanga-zangar.
Kotun kasar Turkiya ta yanke hukuncin daurin rairai kan jagoran kungiyar 'yan awaren kurdawa ta PKK Abdallah Aujalan a cikin shekara ta inda har yanzu ake ci gaba da tsare shi a gidan kaso na kasar, duk kuwa da cewa kasashen yammacin turai suna adawa da wannan mataki da mahukuntan na Turkiya suka dauka.
1053109

captcha