IQNA

An Gina Wasu Makarantu Na Addinin Muslunci A Cikin Wasu Yankuna Na Nigeria

17:38 - July 15, 2012
Lambar Labari: 2369089
Bangaren kur’ani, ana gina wasu makarantun addinin muslunci a wasu yankuna na tarayyar Nigeria da nufin kara fadada harkokin ilimi da al’adunn addini kasantuwar kasa tana daga cikin kasashe da musulmi suka fi yawa a duniya kamar dai yadda kididdiga ta tabbatar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren yada labaransa na nahiyar Afirka cewa, yanzu haka ana gina wasu makarantun addinin muslunci a wasu yankuna na tarayyar Nigeria da nufin kara fadada harkokin ilimi da al’adunn addini kasantuwar kasa tana daga cikin kasashe da musulmi suka fi yawa a duniya kamar dai yadda kididdiga ta tabbatar, wanda kuma daya daga cikin malaman kasar sheikh Hafiz Muhammad said ne ke gudanar da aikin.
A wani labarin kuma Ko shakka babu Amurka ita ce kasa ta farko a duniya da ta yi bakin cikin tunbuke Husni Mubarak daga kan kujerar shugabancin kasar Masar, domin kuwa ta rasa wani babban jigo dake kare munufofinta da na haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin kasashen larabawa da na musulmi, duk kuwa da cewa Amurka ba ta da aboki na din-din-din amma tana da manufa ta din-din-din.
Wasu masu bin diddigin lamurran da suke faruwa na siyasar kasashen larabawa sun imanin cewa, Muhammad Mursi yana da babban kalu bale a gabansa, kasantuwar cewa da dama daga cikin mutanen da suka jefa masa kuri'a suna da fatan ganin ya yanke alakar kasar Masar da haramtacciyar kasar Isra'ila, tare da taimaka ma al'ummar palastinu, sabanin gwamnatin Husni Mubarak da ta kasance babbar kawa ga Isra'ila, da ake hada baki da ita wajen cutar da al'ummar palastinawa.
Bugu da kari kan hakan, wasu daga cikin kasashen larabawa da suke dasawa da Amurka kuma suke kare manufofinta a cikin kasashen larabawa da na musulmi a halin yanzu kamar Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa, ba su lale marhabin da zabar Mursi a matsayin shugaban kasar Masar ba, domin kuwa sun yi iyakacin kokarinsu wajen kasha biliyoyin kudade domin muguda sakamakon zaben na kasar Masar da nufin kayar da Mursi amma hakan bai kai ga nasara ba, wannan ne ma ya sanya Mursi yake kokarin tabbatarwa irin wadannan kasashen larabawa da cewa ba zai mayar da hankali kan abubuwan da suka faru ba, maimakon haka yana neman hadin kansu domin tunkarar gaba.
Yanzu dai za a iya cewa kasashen Amurka da sauran kawayenta larabawa musamman Saudiyya, suna baiwa Mursi rata ne domin su ga kamun luddayinsa, idan har zai iya tafiya da salon siyasa da zai kare manufofinsu, ko da kuwa bai kai kamar yadda babban aminsu Husni Mubarak ya kasance yanayi ba, to za su iya daga masa kafa, a matsayin rashin uwa a kan yi uwa daki. 1050430

captcha