IQNA

Za A Gudanar Da Zaman Taro Na Bayar Da Horo Kan Kur’ani A Kasar Pakistan

17:46 - July 13, 2012
Lambar Labari: 2367320
Bangaren kur’ani, ana shirin fara gudanar da wani shiri na horar da masu koyon karatu da hardar kur’ani mai tsarki kamar dai yadda bangaren kula harkokin kur’ani n amaialkatar addinai ta kasar ta sanar a cikin wani bayani da ta fitar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cewa, ana shirin fara gudanar da wani shiri na horar da masu koyon karatu da hardar kur’ani mai tsarki kamar dai yadda bangaren kula harkokin kur’ani n amaialkatar addinai ta kasar ta sanar a cikin wani bayani da ta fitar a shafin yanar gizo.
A wani bayanin kuma Kotun koli na kasar Pakistan ta yi barazanar tube Priministan kasar mai ci idan shima ya kasa bin umurninta na yin binciken da ya dace kan almundahanar kodaden jama'a wanda ake zargin shugaban kasar ta Pakistan Asif Ali Zardari da yi.
Kamfanin dillancin labaran kasar Farabsa AFP ya bayyana cewa, alkalin kotun Asif Sa'eed Khosa ya aike da wasika ga Priministan kasar Raja Parviz Ashraf a yau Alhamis inda ya bukace shi da ya fara bincike tare da bankin Swizland kan kudaden da ake zargin shugaba Zardari ya ajiye a can, kuma ya bashi nan da ranar 25 ga wannan watan da muke ciki ya aiko masa da sakamakon binciken da ya yi, ko kuma ya fuskanci kora daga kojerarsa kamar yadda ya kori Yusuf Riza Gilani a cikin watan da ya gabata.
Kotun kolin kasar Pakistan dai ta yi watsi da dokar yin afawa ga yan siyasar kasar Pakistan kimani 8000 wanda shugaban kasar Pakistan na lokacin Parviz Musharraf ya yi a cikin watan december shekara ta 2009 kan zargin almundahanan da suka yi da kudaden jama'a. Shugaban kasar Asif Ali Zardari dai yana daga cikin wadanda Musharraf din ya yiwa afwar.
1050319

captcha