IQNA

An Raba Kwafin Kur'ani 1,200 A Masallatai A yankin Sinai Ta Kudu Masar

19:15 - February 24, 2021
Lambar Labari: 3485687
Tehran (IQNA) an raba kwafin kur'ani mai tsarki guda 1200 a yankin Sinai ta kudu ga makaranta kur'ani da kuma masallatai.

Shafin yada labarai na Bawwabah News ya bayar da rahoton cewa, Isma'il Al-rawi wakilin ma'aikatar kula da harkokin addini a yankin Sinai ta kudu, shi ne ya jagoranci raba wadannan kwafin kur'ani mai tsarki a ynakin.

Ministan ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar Muhammad Mukhtar Juma'a ya bayyana cewa, wannan yana daga cikin shirin da ma'aikatarsa take da shi ne na raba kwafin kur'ani guda 20,000 a cikin 'yan kwanakin nan, ga limaman masallatai da kuma makaranta kur'ani a wasu lardunan kasar.

Ya ci gaba da cewa, shirin ba zai takaitu ga masallatai na larduna ba, za a bayar da wasu daga cikin kur'anan ga wasu daga cikin makarantun kasar da suke bukata.

توزیع ۱۲۰۰ نسخه قرآن در میان مساجد و قاریان سینای جنوبی مصر +عکس

توزیع ۱۲۰۰ نسخه قرآن در میان مساجد و قاریان سینای جنوبی مصر +عکس

3955995

 

captcha