Jaridar Daily Sabah ta bayar da rahoton cewa, a cikin lardin Aghari na kasar Turkiya, wata hasumiyar wani tsohon masallaci da ya nutse a cikin ruwa ta yi saura a kan ruwa, inda har yanzu take tsaye ba tare da ta fadi ba.
Wannan lamarin ya faru ne a kauyen Bash Jawish da ke cikin lardin Aghari, bayan gina wata babbar madatsar ruwa, wanda hakan ya yi sanadiyyar nutsewar gine-ginen kauyen da dama, da hakan ya hada har da wani tsohon masallaci da ke yankin.
Babbar koramar da ke yankin ce ta cinye gidaje da sauran gine-gine da suka hada hard a na masallacin, amma abin mamaki shi ne yadda har yanzu hasumiyar masallacin take tsaye.
Wannan yanki dai yana agabashin kasar Turkiya ne, kuam yanki ne da ake fama da sanyi a lokacin hunturu, inda dusar kankara kan rufe yankin baki daya, wannan korama kuma tana daskarewa ta koma kankara har zuwa karshen lokacin hunturu.