IQNA

Ilhan Omar: Musulmin Amurka Suna Da Hakkin Tsayawa Takarar Neman Shugabancin Kasar

19:08 - February 23, 2021
Lambar Labari: 3485683
Tehran (IQNA) ‘yar majalisar dokokin Amurka musulma Ilhan Omar ta bayyana cewa, musulmin Amurka kamar kowa a kasar suna da hakkin tsayawa takarar shugabancin kasar.

Tashar Alarabi Jadid ta bayar da rahoton cewa, Ilhan Omar 'yar majalisar dokokin Amurka musulma Ilhan Omar ta bayyana cewa, musulmin Amurka kamar kowane dan kasa suna da hakkin tsayawa takarar shugabancin kasar bisa doka.

Ilhan ta bayyana hakan ne a zantawarta da tashar ta Alarabi Jadid, inda ta jaddada cewa dole ne gwamnatin Joe Biden ta mike tsaye domin ganin ta aiwatar da abubuwan da ta yi wa mutanen kasar Amurka alkawulla a kansu, daga ciki kuwa hark are hakkokin musulmi a kasar.

Ta ce lokacin shugabancin Trump musulmi sun fuskanci barazana daban-daban, inda hatta ita kanta a matsayinta na ‘yar majalisar dokoki ba ta tsira ba, saboda ita musulma ce, kuma tana saka lullubi a kanta a cikin majalisar dokokin Amurka.

Ilhan ta ce bai kamata a dakatar da gudanar da bincike a kan laifuka daban-daban da Trump ya aikata a lokacin mulkinsa ba, domin kuwa ya cutar da Amurkawa matuka, kamar yadda ya haddasa musu matsaloli a bangarorin tattalin arziki da ma ‘yanci na demokradiyya.

A daya bangaren kuma ta caccaki gwamnatin yahudawan Isra’ila, tare da kiran gwamnatin Joe Biden da ta dauki matakin ganin an taka wa Isra’ila burki, kan gine-ginen matsugunnan yahudawa da take yi a cikin yankunan Falastinawa.

Haka nan kuma ta ce dole ne gwamnatin Biden ta matsa lamba domin ganin an kawo karshen kisan kiyashin da Saudiyya take yi kan al’ummar kasar Yemen.

3955725

 

Abubuwan Da Ya Shafa: laifuka daban-daban Musulmin Amurka
captcha