IQNA

Nasrullah: Yunkurin Makiya Naneman Wargaza Kungiyar Hizbullah Ya Ci Tura

23:50 - February 17, 2021
Lambar Labari: 3485662
Tehran (IQNA) Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, Isra’ila za ta fuskanci martani mafi muni a tarihinta, matukar dai ta yi gigin sake shiga wani sabon yaki da kasar Lebanon

Shafin yada labarai na Al-ahad ya bayar da rahoton cewa, babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, Isra’ila za ta fuskanci martani mafi muni a tarihinta, matukar dai ta yi gigin sake shiga wani sabon yaki da kasar Lebanon.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani jawabi da ya gabatar a daren jiya, babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya jaddada cewa, lokaci ya wuce wanda Isra’ila za ta ci karenta babu babbaka  a kan kasar Lebanon.

Ya ce barazanar da hukumomin Isra’ila suke yi kan yaki mai zuwa tsakaninsu da kasar Lebanon barazana ce, domin kuwa suna da masaniya kan cewa abin da zai biyo baya ba zai yi musu dadi ba, idan kuma har suka yi gigin bude wani sabon yaki kan kasar ta Lebanon, to kuwa Hizbullah za ta mayar da martani da Isra’ila ba ta taba ganin irinsa ba tun daga lokacin kafa ta.

Dangane da matsayar da matsayar da sabuwar gwamnatin Amurka ta dauka na kin amincewa day akin da Saudiyya take kaddamarwa kan al’ummar kasar Yemen kuwa, ya bayyana cewa wannan mataki ne mai kyau, amma hakan sakamako ne na turjiya da al’ummar Yemen suka yi, da kin mika wuya ga ‘yan mamaya.

Haka nan kuma  ya yaba wa kasashen da suka nuna jarunta wajen kin mika wuya ga matsin lambar gwamnatin Trump domin kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila, musamman Aljeriya, Tunisia da kuma Pakistan.

Ya kuma ja hankalin mahukuntan Sudan wadanda suka mika wuya ga matsin lambar Amurka da wasu masu ha’inci daga cikin sarakunan larabawa, da cewa su kwana da sanin cewa, kulla alaka da Isra’ila da suka yi, ba zai taba warware musu matsalolinsu na tattalin arziki ba.

Dangane da batun kafa sabuwar gwamnatin kasar Lebanon kuwa, Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa, kungiyar Hizbullah tana bayar da dukkanin hadin kai da goyon baya, domin ganin an cimma nasara kan hakan.

 

3954532

 

 

captcha