IQNA

Jami’an Tsaron Saudiyya Sun Yi Awon Gaba Da Wata Malamar Addini

23:45 - February 16, 2021
Lambar Labari: 3485659
Tehran (IQNA) jami’an tsaron gwamnatin Saudiyya sun yi awon gaba da wata fitacciyar malamar addini a gidanta da ke garin Makka.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar rahoton cewa, kungiyar kare hakkokin ‘yan adan a kasa Saudiyya da ke da mazauni a wajen kasar ta bayar da bayanin cewa, a jiya jami’an tsaron gwamnatin Saudiyya sun yi awon gaba da wata fitacciyar malamar addini a gidanta da ke garin Makka, inda take koyar da mata ilmomin addini.

Rahoton jami’an tsaron masarautar Al Saud sun kai samame a gidan Malama A’isha Al-muhajiri ‘yar shekaru 65 da haihuwa a garin Makka, inda suka yi awon gaba da ita, kamar yadda kuma suka awon gaba da wasu mutane 20 na daban.

Ita dai wannan mata ta shahara a birnin Makka wajen koyar da ilmomin kur’ani mai tsarki musamman ga mata, haka nan kuma tana yi musu wa’azi a kan abubuwa na addini da kuma sauran lamurra na zamantakewa a mahangar addini.

Babu wani dalili da mahukuntan kasar suka bayar kan yin hakan, amma dai a cikin lokutan baya-bayan nan ana ci gaba da kame malamai a kasar ana maka su gidajen kaso, ko dai saboda banbancin fahimta ta mazhaba, ko kuma saboda ra’yoyinsu kan gwamnatin kasar.

 

3954407

 

 

 

captcha