IQNA

Taro Kan Gudunmawar Mata Wajen Tabbatar Da Sulhu A Duniya

14:52 - February 16, 2021
Lambar Labari: 3485656
Tehran (IQNA) an fara gudanar da zaman taro na kasa da kasa kan irin gudunmawar da mata suke bayarwa wajen tabbatar da sulhu a duniya.

Bisa ga rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar, a jiya ne aka fara gudanar da zaman taron na kasa da kasa kan irin gudunmawar da mata suke bayarwa wajen tabbatar da sulhu a duniya, tare da bayar da gudunmawa wajen kyautata lamurra da suak shafi rayuwar al’umma ta zamantakewa.

Wannan zaman taro yana gudana ne tare da halarta mata masana daga kasashe daban-daban, da suka hada da Lebanon, Syria, Iraki, Afghanistan, Iran, kuma taron yana gudana ne cikin jami’an Zahra da ke birnin Tehran an kasar Iran.

Rabab Hussain Aljaafari wata masaniya ce daga kasar Lebanon da take halartar wanann taro, wadda kuma ta gabatar da jawabi a taron dangane yanayin rayuwar iyalai a cikin kasashen yammacin turai, inda ta bayyana cewa, abubuwa da dama da gwamnatocin kasashen turai suke ikirari a kan kare hakkokin mata ba gaskiya ba ne.

Ta ce akwai abubuwa da dama da suke tabbatar da hakan, daga ciki kuwa hard a yadda ake cin zarafin mata da tozarta su, wanda mace tana da matsayi na musamman da Allah ya ba ta a cikin kowace al’umma, kasantuwar cewa mace ita ce malama ta farko da take gina tarbiya ta iyali tun daga cikin gida.

Ita ma a nata bangaren Hala Sulaiman As’ad, shugabar jami’ar Ummal Arabiyya a kasar Syria ta gabatar da nata jawabin, inda ta bayyana cewa irin gudunmawar da mata suke bayarwa a cikin kowace al’umma tana ga gagarumin tasiri wajen fayyace makomar wannan al’umma.

 

3954287

 

captcha