IQNA

Marine Lepen Ta Sake Yin Kakkausar Suka A Kan Addinin Musulunci

23:34 - February 14, 2021
Lambar Labari: 3485652
Tehran (IQNA) ‘yar takarar shugabancin kasar Faransa mai tsananin kiyayya da addinin musulunci ta sake maimata kalaman kin jinin musulmi.

Jaridar Yeni shafaq ta bayar da rahoton cewa, a cikin wata zantawa a wata tashar talabijin a kasar Faransa, Marine Lepen ‘yar takarar shugabancin kasar mai tsananin kiyayya da addinin musulunci ta sake maimata kalamanta na kin jinin musulmi da kuma addinin musulunci.

Ta ce dole ne gwamnati da kuma al’ummar kasar Faransa su yi aikin sa kai wajen kawo karshen addinin musulunci a cikin fadin kasar Faransa baki daya.

Ta kara da cewa, idan har ta lashe zaben shugaban kasar Faransa, za ta hana gudanar da harkoki na addinin musulunci a kasar, tare da rufe masallatai, da kuma hana mata saka hijabi ko lullubi irin na addinin musulunci, domin wannan sutura ce ta masu tsatsauran ra’ayin musulunci.

A zaben shugaban kasar da aka gudanar a kasar Faransa a cikin shekara ta 2017, Marine Le Pen ta samu kuri’u miliyan 7.6 yayin da Macron ya samu miliyan 8.6.

A zabe zagaye na biyu da aka gudanar kuwa, ta samu kashi talatin da hudu ne cikin dari na dukkanin kuri’un da aka kada, wanda hakan ya bai Macron damar kayar da ita a zaben, inda zabe mai zuwa ake kallon cewa ita ce babbar barazana ga makomar shugabancin Macron a zabe mai zuwa.

3954056

 

captcha